• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Na Matukar Adawa Da Manufar Kariyar Ciniki Da Babakeren Amurka

by CGTN Hausa and Sulaiman
8 months ago
Amurka

LABARAI MASU NASABA

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

Tun ranar 4 ga watan nan da muke ciki, Amurka ta fake da batun maganin Fentanyl, da nufin kakabawa Sin karin harajin kwastam na kashi 10% kan kayayyakin kirar kasar Sin da za ta shigar da su kasar Amurka. Game da wannan mummunan mataki mai sabawa ka’idar cinikin duniya da karya lagon tsarin kasuwanci tsakanin kasashen biyu, ba shakka Sin na matukar adawa da shi, kuma ba za ta zura ido ta rungume hannu tana ta kallo kawai ba. A wannan ranar kuwa, Sin ta mayar da martani, inda da farko ta kai kara a gaban kunigyar cinikin duniya ta WTO kan matakin da Amurka ke dauka, daga baya ta kara kakabawa Amurka harajin kwastam kan wasu kayayyakin da za a shigo da su kasarta, har ma ta shigar da wasu kamfanoni masu ruwa da tsaki cikin jerin sunaye wadanda ba su da aminci a kasar Sin. Jerin matakan da Sin take dauka na mayar da martani sun bayyana niyyar Sin ta kare halastaciyyar moriyarta da kiyaye tsarin cinikin duniya tsakanin mabambantan bangarori, abin da ya zama wajibi kuma ya dace da halin da ake ciki.

To, saboda ganin Amurka tana son nacewa kan batun maganin Fentanyl, ya zama wajibi mu san gaskiya game da batun. Jiya Talata 4 ga watan nan da muke ciki, gwamnatin Sin ta gabatar da takardar bayani kan matakan kayyade maganin Fentanyl ta Sin, inda Sin ta yi bayani kan dimbin ayyuka da take gudanarwa da amfani da fasaha da dabarun da take da shi na kayyade amfani da wannan magani a kasar. Muna iya fahimta daga takardar cewa, Sin daya ce daga cikin kasashen duniya mafi tsauraran manufofi na dakile miyagun kwayoyi da nuna iyakacin kokarin kawar da wannan mummunan aiki tun daga tushe a kasar. A shekarun nan baya, Sin ta amince da matakan da Amurka ke dauka kan batun Fentanyl bisa tunanin jin kai, amma sabanin da fahimtar da Sin take nuna mata, Amurka tana fakewa da wannan batu da nufin matsa mata lamba a bangaren harajin kwastam.

Amurka ba za ta magance matsalar Fentanyl dake dabaibaye kasar ba, sai ta yi shawarwari da bangaren Sin, don daidaita abubuwan dake tsakaninsu. Sin za ta bude kofarta don rungumar shawarwari tsakaninsu, amma idan Amurka tana nufin cimma wata boyayyiyar manufarta ta hanyar yakin harajin kwastam, to Sin za ta mayar da tsattsauran martani ba tare da bata lokaci ba. (Amina Xu)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin
Daga Birnin Sin

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

October 28, 2025
An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas
Daga Birnin Sin

An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

October 28, 2025
Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika
Daga Birnin Sin

Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika

October 28, 2025
Next Post
A Otal Ya Mutu Ba ‘Yan Fashi Ne Suka Kashe Tsohon Kwanturolan NIS Ba – ‘Yansanda

A Otal Ya Mutu Ba 'Yan Fashi Ne Suka Kashe Tsohon Kwanturolan NIS Ba - 'Yansanda

LABARAI MASU NASABA

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe

October 28, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

October 28, 2025
Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

October 28, 2025
An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

October 28, 2025
Gwamna Bago Ya Amince Da Biyan Karin Albashin Naira 20,000 Ga Ma’aikata 

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Hutun Kwanaki 2 Don Zaɓen Ƙananan Hukumomi

October 28, 2025
Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika

Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika

October 28, 2025
Xi Ya Yi Karin Haske Kan Muhimman Shawarwarin Da Kwamitin Kolin JKS Ya Gabatar Yayin Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15

Xi Ya Yi Karin Haske Kan Muhimman Shawarwarin Da Kwamitin Kolin JKS Ya Gabatar Yayin Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15

October 28, 2025
gaza

Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba

October 28, 2025
Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

October 28, 2025
Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

October 28, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.