Kasar Sin ta bayyana matukar adawar ta, da matakin Amurka na harbo wata babbar balan balan na ayyukan fararen hula na kasar Sin, wadda ba ta dauke da matuki.
Wata sanarwar da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya fitar, ta ce bayan tantance bayanai, bangaren Sin ya sha bayyana wa bangaren Amurka cewa, balan-balan din ta shiga sararin samaniyar kasar Amurka ne sakamakon karfin iska da ya karkatar da akalar ta, don haka ko kadan, ba daidai Amurka ta kakkabo ta ba, maimakon haka kamata ya yi Amurka ta kai zuciya nesa, ta aiwatar da matakai bisa kwarewa, da kaucewa fito na fito.
Har ila yau, sanarwar ta ce kakakin ma’aikatar tsaron Amurka ma ya bayyana cewa, balan-balan din ba za ta haifar da wata barazana ga tsaro ko zamantakewar al’ummar Amurka ba.
Karkashin wannan yanayi, Amurka ta yi amfani da karfin tuwo, da aiwatar da matakan da suka wuce gona da iri, wanda hakan ya keta ka’idojin cudanyar kasa da kasa.
A nata bangare, Sin za ta tsaya tsayin daka wajen kare moriyar ta bisa doka, da ’yancin sassan da batun ta shafa. Kaza lika Sin na da ikon daukar matakai gwargwadon hali.
Bugu da kari, yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa game da wannan batu a ranar Juma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin ya ce, ana amfani da balan-balan din ne domin ayyukan binciken yanayi kawai.
Sannan ma’aikatar tsaron Sin ta kuma bayyana matukar adawa da matakin Amurka, na harbo balan-balan din kasar Sin ta ayyukan fararen hula maras matuki.
Wata sanarwar da kakakin ma’aikatar Tan Kefei ya fitar a Lahadin nan, ta bayyana rashin amincewa da matakin Amurka, na yin amfani da karfin tuwo wajen kakkabo balan-balan din.
Tan ya ce “Mun gabatar da matukar rashin amincewa da matakin na Amurka, kuma muna da ikon daukar matakan da suka wajaba na shawo kan makamancin wannan yanayi”. (Saminu Alhassan)