Wani kundin bayanai da kungiyar makamashin nukiliya ta Sin ko CNEA ta fitar a yau Laraba, ya nuna yadda kasar Sin ta zama a kan gaba a duniya, a fannin gina cibiyoyin sarrafa lantarki ta amfani da makamashin nukiliya.
A cewar kundin, a halin yanzu, Sin na kan ginin irin wadannan cibiyoyi guda 24, wadanda ke iya samar da lantarki da karfin sa ya kai kilowatts miliyan 26.81.
Hakan ya tabbatar da matsayin kasar Sin, na wadda ke gudanar da cibiyoyin ta na sarrafa nukiliya domin samar da makamashi, bisa tsaro da daidaito a tsawon lokaci, a lokaci guda kuma, tana kara gina sabbin cibiyoyin cikin nasara. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)