Sakatariyar kwamitin JKS na babbar hukumar kwastam ta kasar Sin Sun Meijun, ta bayyana a taron hukumomin kwastam na kasar a ranar 7 ga wata cewa, darajar cinikin waje na kasar Sin ta zarce manufar da aka tsara ta yuan triliyan 43 a karon farko a shekarar 2024, inda ta karu da kashi 5 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar 2023, kuma ta ci gaba da rike matsayinta na kasa mafi girma a fannin cinikin kayayyaki a shekaru takwas a jere.
A shekarar 2024, an fuskanci karuwar rashin tabbas da rashin zaman lafiya a waje, duk da haka hukumar kwastam ta samar da hidimomi mafi kyau domin saukake da sa kaimi ga inganci da daidaiton yawan cinikin waje na kasar Sin. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)