Hukumar kula da harkokin likitanci da magungunan gargajiyar kasar Sin ta fitar da bayanin cewa, kasar Sin za ta inganta harkokin gina sassan likitancin gargajiya na kasar da za su zamo kan gaba a matakinsu, domin kara ingancin aikin jinya a asibiti. Kana, ya zuwa shekarar 2029, za a kafa cikakken tsarin jinya ta fasahohin gargajiyar Sinawa, kuma ana sa ran sassan jinya na fasahohin gargajiyar kasar su kai kimanin dubu 10 zuwa wannan shekara.
Bayanin ya kara da cewa, sassan jinya na fasahohin gargajiyar Sin masu inganci za su zama wani sashi mai muhimmanci, wajen nuna kwarewar fasahohin, da nuna ingancin ayyukansu na jinya, da kuma ba da gagarumar gudummawa ga kiwon lafiyar al’umma kamar yadda ake fata.
A watan Mayu na bana, hukumar kula da harkokin likitanci da magungunan gargajiyar kasar Sin ta zabi asibitoci guda 1073, wadanda suke kan gaba a fannin jinya ta fasahohin gargajiyar kasar, inda ta sanya su a jerin masu inganci. A halin yanzu kuma, galibin sassan jinya na fasahohin gargajiyar kasar sun kasance sassa masu muhimmanci a wadannan asibitoci. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp