A ranar 24 ga watan Yunin shekarar 2022, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya karbi bakuncin babban taron tattaunawa kan ci gaban duniya, inda ya gabatar da matakai na hadin gwiwa a aikace guda 32 da Sin za ta dauka, don tabbatar da shawarar raya kasa da kasa, wadanda suka samu goyon baya da martani mai kyau daga al’ummomin kasa da kasa. A gabannin ranar cika shekara guda da gudanar da taron, cibiyar ilmin raya kasa da kasa ta kasar Sin ta fitar da rahoton ci gaban da aka samu kan aiwatar da shawarar raya kasa da kasa.
Game da haka, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao ning ta bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba yi a yau Talata cewa, kasar Sin tana maraba da bangarori daban daban da su kara mayar da hankali da ba da goyon baya ga shawarar raya kasa da kasa, kuma a shirye take ta yi aiki tare da kasashen duniya wajen sa kaimi ga yin hadin gwiwa mai dorewa a kan shawarar, da ba da gudummawa wajen gaggauta aiwatar da ajandar samun dauwamamman ci gaba ta MDD nan da shekarar 2030. (Mai fassara: Bilkisu Xin)