Jiya Litinin da safe, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasser Kanaani ya bayyana a gun taron manema labarai na yau da kullum da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta shirya cewa, bisa sanarwar hadin gwiwa da ministocin harkokin wajen kasashen Iran da Saudiyya suka fitar a birnin Beijing, kasashen biyu sun maido da harkokin diflomasiyya a tsakaninsu a hukumance. Ya ce tawagar wakilan Saudiyya sun isa birnin Tehran, hedkwatar kasar a ran 8 ga wata, kuma ya zuwa yanzu suna kokarin gudanar da harkoki masu nasaba da sake bude ofisoshin jakadancin Saudiyya dake Tehran da Mashhad.
A ‘yan kwanaki masu zuwa ne, ake sa ran tawagar Iran za ta tafi kasar Saudiyya, domin fara aikin bude ofishin jakadancin.
Nasser Kanaani ya darajanta muhimmiyar rawar da Sin take taka wajen farfado da huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu. Ya ce, “Iran da Saudiyya sun kai ga cimma wannan muhimmiyar yarjejeniya ce, bisa taimako da aniyyar da Sin take da su, kamar yadda aka bayyana a cikin wannan hadaddiyar sanarwa, rawar da Sin ta taka kan wannan batu, tana da ma’ana kuma mun yaba da hakan”. (Amina Xu)