Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta bayyana cewa, kakaba haraji da sauran shingayen kasuwanci ba za su amfani kowa ba, kuma suna matukar haifar da illa ga samar da wadatar tattalin arzikin duniya, da tafiyar da shi cikin kwanciyar hankali.
Jami’ar wacce ta bayyana haka a yau Alhamis yayin wani taron manema labarai, ta ce kasar Sin za ta ci gaba da kara bude kofa ga kasashen waje, da nuna goyon baya ga ka’idojin ciniki cikin ‘yanci, da tsarin kasuwanci a tsakanin bangarori daban-daban, da karfafa samun moriyar kasa da kasa ta fuskar tattalin arzikin da ya hade kowa da kowa, da neman bunkasa ta bai-daya, tare da samar da moriyar juna da dukkan kasashen duniya.
- Wa Ke Dandana Kudar Matakin Harajin Kwastan Da Gwamnatin Amurka Ta Dauka
- Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 84, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 3 A Katsina
Mao ta bayyana hakan ne a matsayin martani ga sabon rahoton hasashen tattalin arziki na wucin gadi na kungiyar bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki da ci gaban kasashe ta OECD, wanda ya rage hasashen matakin ci gaban da za a samu a duniya. Rahoton ya yi nuni da cewa, shingayen kasuwanci na baya-bayan nan da wasu kasashe suka kafa na iya kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin duniya, da kuma haifar da hauhawar farashin kayayyaki.
Bugu da kari, a cewar rahotannin kafofin yada labarai, wani dan siyasa a majalisar dokokin Amurka ya aike da wasiku zuwa jami’o’in Amurka shida, inda ya bukaci a bayar da bayanai kan dalibansu Sinawa saboda abin da ya shafi batun “tsaron kasa”. Sai dai, Mao ta bukaci Amurka da ta guji daukar matakan nuna wariya da takura wa daliban kasar Sin. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp