Yau Alhamis, an fara jigilar kayayyakin aikin jinya da za su biya bukatun mutane 5000 daga birnin Beijing na kasar Sin zuwa kasar Syria, wadanda suka kasance agajin jerin farko da kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta kasar Sin ta samar wa yankunan kasar Syria, wadanda bala’in girgizar kasa ya ritsa da su.
Bayan barkewar mummunar girgizar kasa a kasashen Turkiye da Syria, a ranar Litinin da ta gabata, kungiyar Red Cross ta kasar Sin ta fara daukar matakai ba tare da wani jinkiri ba. Ta riga ta ba kungiyoyin Red Crescent na kasashen 2 tallafin kudi, inda kowaccensu ta samu dalar Amurka dubu 200. Haka zalika, kungiyar na ci gaba da lura da bukatun da ake samu a yankunan kasashen da Iftila’in ya ritsa da su, tare da samar da dauki gwargwadon karfinta.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning, ta gabatar da yadda kasarta take kokarin samar da tallafi ga kasashen Turkiyya da Siriya da iftila’in girgizar kasa mai karfin gaske ya shafa, inda ta ce, baya ga kudade da tallafin kaya, kasar na gaggauta aikin samar da tallafin abinci ga Siriya, ciki har da alkama ton 220 dake kan hanya, da kuma shinkafa da alkama sama da ton 3000 da za’a yi jigilarsu nan bada jimawa ba.
Mao ta ce, jim kadan bayan isarsu Turkiyya, ma’aikatan ceto na kasar Sin suka fara ayyukan ceto a birnin Antakya na jihar Hatay il inda bala’in ya fi yi wa muni, kuma bisa hadin-gwiwa da takwarorin su na kasar Turkiyya, sun ceto wata mata mai juna biyu daga baraguzan wani gini da sanyin safiyar yau Alhamis. Kana, da daren jiya Laraba, gwamnatin yankin Hong Kong na kasar Sin ita ma ta tura wata kungiya mai ma’aikatan ceto 59 zuwa Turkiyya don samar da taimako. Har ila yau, da safiyar yau Alhamis, an soma jigilar kayayyakin aikin jinya da za su biya bukatun mutane 5000 daga birnin Beijing na kasar Sin zuwa kasar Siriya, wadanda suka kasance agaji jerin farko da kungiyar bada agaji ta Red Cross ta kasar Sin ta samar wa yankunan kasar Siriya, wadanda bala’in girgizar kasa ya ritsa da su. Ma’aikatan ceto na kungiyar Red Cross ta kasar Sin su ma sun tafi Siriya. (Bello Wang, Murtala Zhang)