An yi bikin kaddamar da shirin tallafin abinci na kasar Zambia, wanda Sin ta bayar da kudin aiwatarwa ta hannun asusun raya kasashe da hadin gwiwar kasashe masu tasowa, da hadin gwiwar shirin samar da abinci na MDD (WFP) jiya Litinin a birnin Lusaka.
Karkashin shirin, Sin ta samar da taimakon dala miliyan 3.5 domin taimaka wa Zambia sayen kimanin metric ton 5,641 na masarar da aka noma a kasar. Za a raba masarar cikin watanni 3 ga mutane 188,057 ko kimanin iyalai 37,000, a wuraren da suka fi fama da matsalar fari a lardunan kudanci da yammacin kasar.
Bikin mika tallafin ya samu halartar jakadan Sin a Zambia Han Jing da mataimakin shugaban kasar Mutale Nalumango da jami’an ofishin jakadancin Sin da sauran wakilan gwamnatin kasar tare da wakilan cibiyar musayar kwarewa da tattalin arziki ta kasa da kasa ta Sin da na shirin WFP, wadanda su ne abokan hulda masu aiwatar da shirin. (Mai fassara: Fa’iza)