Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Tan Kefei, ya bayyana matukar adawar kasar Sin, da yadda wasu kasashe suka kara adadin kudaden da suke kashewa a fannin ayyukan soji, karkashin manufar da suka kira “Dakile barazanar ayyukan sojin kasar Sin”.
Tan Kefei, ya ce har kullum Sin na aiwatar da manufofi ne na wanzar da zaman lafiya, wanda hakan ke taimakawa matuka wajen tabbatar da doka da oda a duniya baki daya. Kaza lika ga ragowar sassan duniya, Sin ta zama ginshikin samar da damammaki ba wai kalubale ba.
Jami’in ya kara da cewa, Amurka ta kasance a sahun gaba tsakanin kasashen duniya, a fannin yawan kasafin kudin ayyukan soji, a hannu guda kuma, ita ce kasar dake ingiza yake-yake da haifar da rudani. Har ila yau, Amurka ce babbar barazana ga zaman lafiyar duniya, da tsaro da daidaito. A sa’i daya kuma, Sin na kira ga Birtaniya da ta rungumi halayya ta gari, ta yi wa kasar Sin kyakkyawar fahimta, ta kuma dakatar da yayata zargin da ake yi wa kasar Sin, na kasancewa barazana ga saura.
Game da batun hadin gwiwar da Amurka da Birtaniya da Australia ke yi wajen kirar jirgin karkashin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya kuwa, Tan ya ce Sin na matukar adawa da wannan hadin gwiwa da kasashen 3 suka kira da “Hadin kai a fannin tsaro”.
Ya ce, irin wannan karamar gamayya da aka gina kan tunani irin na cacar baka, ba za ta haifarwa kowa da mai ido ba. A nata bangare kuwa, Sin na fatan kasashen da batun ya shafa za su lura da salon ci gaba na wannan zamani, su yi watsi da son kai don cimma moriyar su, su kuma saurari kiraye-kirayen sassan kasa da kasa da budaddiyar zuciya, kana su sauke nauyin dake wuyan su na cudanyar kasa da kasa, tare da ba da karin gudummawa wajen wanzar da zaman lafiya, da daidaito a dukkanin shiyyoyi. (Saminu Alhassan)