Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Sun Lei, ya gabatar da tsokaci dangane da daftarin da Amurka ta gabatar, game da bukatar tsawaita ayyukan tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a yankin Abyei na ko UNISFA a takaice. Sun, wanda ya yi tsokacin a jiya Juma’a, bayan jefa kuri’a a zaman kwamitin tsaron MDD kan daftarin, ya ce kasarsa ta damu game da yadda Amurka ta ingiza daftarin, wanda da ma ita ce ta gabatar da shi.
Ya ce a matsayin kasar dake sahun gaba wajen tallafawa tawagar ta UNISFA, Sin ta shiga an dama da ita a shawarwarin da suka shafi daftarin, to sai dai kuma daftarin ya fitar da wasu ma’aunai masu alaka da yanayin gudanar da harkokin siyasa a yankin na Abyei, tare da hade hakan da makomar tsawaita wa’adin aikin tawagar UNISFA. Kasar Sin ba ta gamsu da hakan ba, don haka ta kauracewa jefa kuri’a kan daftarin.
Sun Lei ya kara da cewa, yayin tattaunawa kan daftarin, da dama daga membobin kwamitin tsaron MDD sun gabatar da shawarwari masu ma’ana domin sake nazari. Kana a yayin shawarwarin ranar Alhamis a zauren kwamitin tsaron, dukkanin sassa sun amince kasar da ta gabatar da daftarin, ta shigar da shawarwarin dukkanin bangarori, maimakon rufe ido da ingiza shi yadda ta ga dama.
Ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da sauran membobin kwamitin tsaron MDD, wajen wanzar da hadin kai, da kawance tsakanin sassan kwamitin na tsaro, ta yadda za a kai ga tabbatar da tawagar ta musamman ta cimma nasarar sauke alhaki da nauyin dake wuyanta, da ma kara azamar wanzar da zaman lafiya, da tsaro a matakin kasa da kasa da na shiyyoyi. (Saminu Alhassan)














