Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin ta bayyana matukar adawa ga matakin kungiyar tarayyar Turai EU, na sanya takunkumi kan wasu kamfanonin Sin, ta hanyar fakewa da rikicin Rasha da Ukraine.
Lin Jian, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na Talatar nan, ya ce har kullum kasar Sin na bayyana rashin amincewa da takunkuman kashin kai da wani bangare ke dauka, ba tare da la’akari da tabbatattun ka’idojin cudanyar kasa da kasa ba, kana ba tare da amincewar kwamitin tsaron MDD ba. Kasar Sin ta nuna matukar bacin ranta da takunkuman na EU, ta kuma sanar da bijirewar ta da hakan.
- Nijeriya Ta Samu Sama da N181bn Daga Wutar Lantarkin Da Ta Sayarwa Kasashen Waje
- Maguire Na Son Sabunta Kwantiraginsa A Manchester United
Lin Jian ya ce, “Game da batun Ukraine, a ko da yaushe kasar Sin na kokarin ganin an cimma nasarar samar da zaman lafiya da komawa teburin shawarwari, kuma ba ta taba samar da makamai ga daya daga sassan biyu dake rikici da juna ba, kana tana dagewa wajen kiyaye bazuwar abubuwan da ake iya amfani da su a ayyukan fararen hula da na soji, tare da lura da tantance adadin jirage marasa matuka da ake fitarwa daga kasar zuwa sassan duniya.
To sai dai kuma, Sin na ganin bai dace a katse, ko a gurgunta musaya da hadin gwiwa da aka saba tsakanin kamfanonin Sin da na Rasha ba. Duba da cewa a halin da ake ciki ma, mafi yawan kasashen duniya, ciki har da na Turai da Amurka, na ci gaba da gudanar da cinikayya tare da Rasha.
Don haka Sin ke kira ga sassan Turai, da su kaucewa daukar matsaya biyu a harkokin hadin gwiwar raya tattalin arziki da cinikayya da Rasha, su dakatar da kokarin bata sunan kasar Sin ba tare da sahihan dalili ba, da kauracewa lahanta halastattun hakkoki, da moriyar kamfanonin kasar Sin. Kaza lika, Sin za ta aiwatar da matakai na wajibi, don tabbatar da kare halastattun hakkoki da moriyar kamfanoninta. (Saminu Alhassan)