Hukumomin kasar Sin sun fitar da wani shiri a ranar Laraba, 9 ga watan nan, domin inganta sha’anin kiwon lafiya, a yayin da kasar ke kokarin habaka ingancin kayayyaki da ayyukanta na kiwon lafiya, da kuma biyan bukatun jama’a da ke kara yawaita bisa yadda suke neman samun ingantacciyar rayuwa.
Domin karfafa kashe kudi ta wannan fannin, kasar Sin za ta kara kyautata ingancin lafiyar abincin mutane, da habaka samar da abinci na musamman a kasuwanni a karkashin shirin, wanda ma’aikatar kasuwanci ta kasar da wasu ma’aikatun gwamnati 11 suka tsara.
Kazalika, za a karfafa samar da kayan amfanin gona masu inganci, sannan za a fatattaki abubuwan da ake karawa a abinci ba bisa ka’ida ba, kamar yadda aka tsara.
Haka nan, an tsara yadda za a nuna wa cibiyoyin kiwon lafiya hanyoyin fahimtar da mutane ire-iren abinci da motsa jikin da suka dace, musamman ma ga masu fama da hawan jini, da siga, da muguwar kiba da sauran lalurorin rashin lafiya.
Bugu da kari, a karkashin shirin, kasar Sin ta sha damarar samar da karin yanayin motsa jiki da na wasanni, da bunkasa harkokin yawon shakatawa ta fuskar wasanni. Za a kuma gaggauta kawo sauye-sauye da daga darajar masana’antun kera kayayyakin wasanni ta hanyar amfani da manhajojin fasahohi da fikirar zamani. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp