Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin na nuna adawa da matakin Amurka na keta ikonta na teku a tekun kudancin kasar Sin, tare da nuna goyon baya ga kasar Philippines da ta keta hakkin kasar Sin.
Kakakin ya kara da cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta daina amfani da batun tekun kudancin kasar Sin wajen haifar da rashin jituwa tare da mutunta cikakkun yankuna da na tekun kasar Sin. (Mai fassara: Yahaya)