Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya musanta kalaman karya da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi cewa, wai “Sin ta kai hari da balan-balan” a yayin taron manema labarai da aka saba shirya Larabar nan. Inda ya bukaci bangaren Amurka da ya nuna gaskiya, da gyara kura-kuranta, fuskanta tare da magance barnar da ta haifarwa alakar Sin da Amurka ta hanyar amfani da karfi.
Ya kara da cewa al’amura da dama sun nuna cewa, fashewar bututun iskar gas na “Nord Stream” ba hatsari ba ne, amma abu ne da gangan.
Wang Wenbin ya ce, Amurka da sauran kasashen NATO su ne kan gaba wajen samar da makamai a yakin da Ukraine ke yi, amma a kullum suna yada yiwuwar kasar Sin za ta iya baiwa Rasha makamai. An yi amfani da irin wadannan dabaru da kuma kitsa su a farkon rikicin Ukraine. (Mai fassarawa: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp