Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, hadin gwiwa a bangaren ilimi tsakanin Sin da Amurka na moriyar juna ne, kuma Sin ta kasance mai adawa da siyasantar da hadin gwiwar bangaren ilimi.
Kakakin ma’aikatar Mao Ning ce ta bayyana haka yayin taron manema labarai na yau Juma’a, lokacin da aka nemi jin ta-bakinta kan matakin gwmnatin Trump na hana jami’ar Harvard daukar dalibai daga kasashen waje.
A cewar Mao Ning, ire iren wadannan matakai da Amurka ke dauka za su lalata kima da darajar kasar, tana cewa, Sin za ta nace wajen kare hakkoki da muradun dalibai da malaman kasar dake kasashen waje.
Ta kuma jaddada adawar Sin ga bata sunanta da takalarta ba gaira ba dalili, tana mai kira ga Amurka ta dage takunkumanta da suka sabawa doka. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp