Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun, ya bayyana a yau Laraba cewa, idan har da gaske ne Amurka ke son warware batutuwan da suka shafi karin harajin kwastam tare da kasar Sin ta hanyar tattaunawa da yin shawarwari, to dole ne ta daina yin barazana da tatsar kudi, kuma ta hau teburin shawarwarin bisa daidaito, da mutunta juna da kuma la’akari da muradun juna.
Guo Jiakun ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai na yau da kullum, a wani bangare na martani ga sabbin kalaman da shugaban Amurka Donald Trump da Sakataren baitulmalin kasar Scott Bessent suka yi game da takun-sakar kasuwanci da ake yi a tsakanin kasashen biyu.
- Rashin Tsaro: Tinubu Ya Gana Da Shugaban Tsaro Da Ribadu Kan Kashe-kashen Rayuka
- Rashin Jituwa Tsakanin Amurka Da China Na Iya Jefa Tattalin Arziƙin Duniya Cikin Hatsari – IMF
Ya ce, tun ba yau ba, kasar Sin ta riga ta yi nuni da cewa, babu wanda zai yi nasara a yakin kasuwanci da karin harajin kwastam, kuma matakin kariyar ciniki ba zai kai kowa ko ina ba, inda ya kara da cewa warware hadin gwiwar hada-hadar cinikayya da wargatsa tsarin samar da kayayyaki ba za su haifar da komai ba illa mayar da wanda ya haddasa saniyar ware.
Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin ba ta son gwabza yakin kasuwanci da karin harajin kwastam, amma kuma ba za ta rungume hannu ta zuba ido ba idan yakin ya kaure, yana mai nuni da cewa, idan har Amurka ta zabi fafata yakin kasuwanci, Sin za ta sha damarar yakin har sai ta ga abin da ya ture wa buzu nadi. Sai dai kuma duk da haka, ya ce idan Amurka na son a tattauna, Sin za ta bar kofarta a bude domin yin hakan.
Bugu da kari, dangane da batun yadda a baya-bayan nan kafafen yada labarun kasar Panama suka soki Amurka kan yin katsalandan da nuna babakere a kasashen yankin tsakiyar Amurka, musamman a kasar ta Panama, inda suka zargi Amurkar da yunkurin karbe ragamar mashigin ruwan Panama ta hanyar fakewa da wai “barazanar kasar Sin” wadda babu ita kwata-kwata. Guo Jiakun ya mayar da martani inda ya ce, bayanan da kafafen yada labarai na Panama suka yi sun fallasa ainihin halin Amurka na babakere.
Guo ya kara da cewa “Babu wata karya da za ta iya lullube ungulu da kan zabon Amurka a kan burinta na neman karbe akalar mashigin ruwan Panama”. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp