Jami’i mai kula da muhalli da halittun kasar Sin, ya bayyana a jiya Laraba cewa, Sin ta cimma burin rage fitar da yawan iskar carbon mai dumama yanayi kafin shekarar 2030, ta hanyar bin tsarin MDD, wato taka rawa gwargwadon karfin kasa bisa halin da take ciki.
Wannan tsari da majalisar ta gabatar bisa yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi na MDD, ya tanaji mambobi su tsaida muradunsu gwargwadon karfinsu da halin da suke ciki. A nata bangare buri na kasar Sin shi ne tabbatar da kaiwa matsayin kolinta na fitar da iskar carbon mai dumama yanayi kafin shekarar 2030, tare da fatan cimma daidaito tsakanin yawan iskar carbon da za ta fitar da yawan abubuwan da za su shawo kan tasirin iskar kafin shekarar 2060.
Rahotanni na cewa, Sin tana tattaunawa kan sabon burinta a majalisar, kuma za ta yi aiki gwargwadon karfinta, bisa la’akari da halin da take ciki, don gabatarwa ofishin sakataren yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi na majalisar a shekarar 2025 kudurin da ta tsaida bisa yarjejeniyar Paris, da yarjejeniyar UAE da aka kulla a shekarar bara. (Amina Xu)