Yau Litinin ofishin ‘yan jarida na kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai don bayyana nasarorin da Sin ta samu a fannin ban ruwa a lokacin “shirin raya kasa na 14 na shekaru biyar” . Minista mai kula da harkokin ban ruwa Li Guoying ya bayyana cewa, tun daga farkon shirin, Sin ta fara samun ci gaba mai yawa a fannin gina kayayyakin ban ruwa.
A shekarar 2022, kudaden da aka kashe wajen gina ayyukan ruwa sun kai sama da RMB yuan tiriliyan 1 a karon farko, kuma sun ci gaba da kafa tarihi har tsawon shekaru 3. A shekarar 2024, kudaden sun kai tiriliyan 1.3529 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 190. Kuma ana sa ran yawan kudaden da za su shafi aikin ban ruwa a wa’adin shirin za su kai fiye da yuan tiriliyan 5.4, kwatankwacin fiye da dalar biliyan 758, wanda ya ninka sau 1.6 bisa na shirin raya kasa na 13.
Zuwa karshen shekarar 2024, Sin ta gina madatsun ruwa 95,000, ta gudanar da manyan ayyukan karkatar da ruwa 200, da samar da manyan filayen ban ruwa guda 6,924, da kuma gina magudanan ruwa da jimilar tsawonsu ta kai kilomita 318,000. Wannan ya sa Sin ta zama kasa mafi girma a duniya dake da tsarin ban ruwa mafi inganci dake kuma amfanawa mutane mafi yawa.
Bugu da kari, Li Guoying ya bayyana cewa, ana sa ran a karshen shiri na 14, yawan filayen da tsarin ban ruwa na kasa zai shafa, zai kai kashi 80.3%, kuma filayen ban ruwa za su kai hekta fiye da miliyan 72.6, kana yawan kauyuka masu ruwan famfo zai kai kashi 96%. Wannan ya ba da tabbacin samar da ruwa wajen aiwatar da manyan manufofin kasa, da samar da amfanin gona, da jin dadin al’ummar birane da kauyuka. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp