Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a taron manema labarai na yau da kullum yau Litinin din nan cewa, kasar Sin ta damu matuka da girgizar kasar da ta auku a kasar Morocco, kuma tana son ci gaba da taimakawa kasar Morocco bisa bukatunta.
Mao Ning ta bayyana cewa, a kokarin ganin an taimakawa kasar Morocco wajen tinkarar mummunan iftala’in girgizar kasar da ta afkawa kasar, kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin ta sanar da cewa, za ta baiwa kungiyar agaji ta Red Crescent ta kasar Morocco taimakon gaggawa na tsabar kudi har dalar Amurka dubu 200.
Kana hukumar kula da harkokin hadin gwiwa da raya kasa ta duniya ta kasar Sin ta bayyana cewa, a shirye take ta ba da agajin gaggawa bisa la’akari da bukatun wadanda lamarin ya shafa na Morocco.
Kasar Sin tana son ci gaba da taimakawa Morocco bisa bukatunta.(Ibrahim)