A matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga cimma matsaya da ma fara aiki da yarjejeniyar Paris, kana kasar Sin tana yin kokarinta wajen cimma buri a wannan fanni a dogon lokaci. Kasar Sin ta riga ta maida manufar tinkarar sauyin yanayi a matsayin manufar kasar, ta kuma dauki matakan raya makamashin da ake iya sabuntawa, da kafa tsarin kiyaye kaiwa ga fitar da kololuwar sinadarin cabon, da daidaita yawan gurbatacciyar iska da ake fitarwa da wanda ke cikin iska ta hanyoyin shuka itatuwa da rage fitar da gurbatar iska da sauransu, da sa kaimi ga kyautata tsarin masana’antu da makamashi da sufuri, da kafa kasuwar sinadarin cabon mafi girma a duniya domin fitar da iskar dake dumamar yanayi da sauransu, don haka yawan carbon dioxide da kasar Sin ta fitar a shekarar 2022 ya ragu da kashi 51 cikin dari ko fiye bisa na shekarar 2005.
Aiwatar da ra’ayin bangarori daban daban bisa tushen MDD, da amsa kiran kasashe masu tasowa, da yin hadin gwiwa wajen kyautata tsarin raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba, su ne hanyoyin tinkarar sauyin yanayi da dan Adam suke bi. Kasar Sin za ta ci gaba da samar da gudummawarta wajen daidaita matsalolin yanayin duniya, da yin kokarin cimma burin kiyaye fitar da kololuwar sinadarin cabon kafin shekarar 2030, da daidaita yawan gurbatacciyar iska da ake fitarwa da wanda ke cikin iska ta hanyoyin shuka itatuwa da rage fitar da gurbatar iska da sauransu kafin shekarar 2060, kasar Sin za ta cika alkawarinta a wannan fanni. (Zainab)