A yau Laraba, ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta sanar da cewa, kasar ta kara wasu bankuna biyu na kungiyar tarayyar Turai UAB Urbo Bankas da kuma AB Mano Bankas, a cikin jerin sunayen wadanda ta dauki matakan mayar da martani a kansu.
An dauki matakan ne a matsayin martani ga matakin EU na shigar da wasu cibiyoyin kudi na kasar Sin guda biyu cikin jerin wadanda aka kakaba wa takunkumi a karkashin takunkuman da ta kakaba wa kasar Rasha a watan Yuli.
Ma’aikatar ta bayyana cewa, matakin na EU ya saba wa dokokin kasa da kasa, da kuma muhimman ka’idojin huldar kasa da kasa, tare da kawo cikas ga halastattun hakkoki da muradun kamfanonin kasar Sin. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)