Sashin kula da kandagarkin COVID-19 na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya kira taron manema labarai a yammacin yau, inda mai magana da yawon hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin Mi Feng ya yi bayani cewa, tun barkewar annobar, Sin ta dauki matakai daban-daban na hada likitancin yamma da na gargajiya ta kasar Sin wajen guda, da amfani da magungunansu baki daya, wannan ya sa aka yi amfani da fifikon likitanci da magungunan gargajiya na kasar Sin yadda ya kamata. Matakin da ya kara yawan mutanen da suka warke daga cutar da kuma rage yawan masu kamuwa da rashin kafiya mai tsanani, da yadda masu kamuwa da cutar za su warke cikin hanzari.
A halin yanzu, aikin riga kafin cutar na kasa, ya sauya daga hana kamuwa da cuta zuwa kare lafiyar jama’a da kare su daga kamuwa da cututtuka masu tsanani. Kauyuka na daga cikin wuraren da za a mai da hankali a kai, kuma mutanen da suke fi jawo hankali su ne tsoffi da masu juna biyu da kananan yara da wadanda ke fama da wasu cututtuka.(Amina Xu)