Kamfanin mai na kasar Sin (CNOOC) ya bayyana cewa, an fara aiki da wurin ajiyar iskar carbon na farko a tekun kudancin kasar Sin jiya Alhamis.
A cewar kamfanin, an tsara aikin ne da nufin adana jimillar sama da tan miliyan 1.5 na carbon dioxide (CO2), wanda ya yi daidai da dasa itatuwa kusan miliyan 14.
Aikin yana tattara da sarrafa carbon dioxide daga rijiyoyin mai, sannan kuma a cusa su cikin wani zurfin kusan mita 800 a karkashin teku da kuma kusan kilomita 3 daga dandamalim bisa tsarin na kimiyya.
Gudanar da aikin na nuni da nasarar da kasar Sin ta samu, wajen samun cikakkun fasahohi da na’urori don tattarawa, da sarrafawa, da cusawa, da adanawa da ma kula da sanadarin carbon dioxide a cikin teku.
A cewar kamfanin, hakan ya bude wani sabon babi na nasara ga kasar Sin, a kokarin cimma burinta na rage fitar da hayakin carbon dioxide nan da shekarar 2030, da kuma daidaita hayakin na carbon dioxide nan da shekarar 2060. (Mai fassarawa: Ibrahim)