Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta fitar da wata doka ta mayar da martani da za ta shafi wasu kungiyoyi da jami’ai na kasar Canada. An fitar da dokar ne a ranar Asabar 21 ga watan nan, kuma ta fara aiki tun daga ranar.
Bisa tanadin dokar dake karkashin sassan na 3, da 4, da 5, da 6, da 9 da 15 na dokokin shari’ar janhuriyar jama’ar kasar Sin, mai nasaba da mayar da martani ga takunkuman kasashen ketare, Sin ta yanke shawarar daukar wasu matakai da suka hada da daskarar da kadarorin wasu kungiyoyi da jami’an kasar Canada.
- Rushewar Gini Ya Kashe Rayuka 4, An Ceto Mutane 105 A Abuja A 2024 – FEMD
- Kamfanin Jiragen Sama Na Azman Ya Musanta Zargin Sayar Da Jiragensa Ga Iran
Sassan da matakin daskararwar zai shafa, sun hada da kadarorin da ake iya sauyawa wuri da wadanda ba a iya daukewa, da wasu sauran kadarorin dake cikin kasar ta Sin, mallakin kungiyoyin “Uyghur Rights Advocacy Project”, da na “Canada-Tibet Committee” da na jami’ansu. Kaza lika, an haramtawa duk wasu kungiyoyi, da daidaikun jama’a dake cikin kasar Sin yin kowace irin mu’amala, ko hadin gwiwa da sauran harkoki tare da su.
Har ila yau, ba za a baiwa jami’ai masu nasaba da kungiyoyin biyu biza ta shiga ko fita daga kasar Sin ba, cikin har da yankunan musamman na Hong Kong da Macao. (Saminu Alhassan)