Kasar Sin ta fitar da wasu ka’idoji da za su taimaka, wajen fadada, da bunkasa kasuwannin cikin gidan kasar, ta yadda hakan zai taimaka ga ci gaban bukatun hajoji a cikin gida na tsawon lokaci.
Ka’idojin wadanda kwamitin kolin JKS, da hadin gwiwar majalissar gudanarwar kasar suka fitar, za a aiwatar da su ne har zuwa shekarar 2035, inda ake sa ran za su taimaka, wajen daga matsayin cinikayyar cikin gida da zuba jari, tare da kafa tsari mai karfi na bunkasa bukatun hajoji a cikin kasar.
Domin cimma wannan manufa ta dogon lokaci, Sin ta shirya tsare-tsare, na fadada cinikayya a gida, da inganta matakan rarraba hajoji, da kyautata ingancin hajojin dake shiga kasuwa, da kara inganta tsarin gudanar da kasuwanni, da tafiyar da harkokin tattalin arziki, karkashin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14, wanda zai gudana tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025.
Bugu da kari, ana sa ran karkashin sabbin ka’idojin, Sin za ta zage damtse wajen bunkasa wadatar bai daya, domin cimma moriya daga bukatun kasuwannin cikin gida, da ma daga matsayin tabbacin kasuwar hada-hadar hannayen jari na kasar, domin karfafa tushen ci gaban kasuwannin cikin gidan kasar. (Saminu Alhassan)