Kwamitin kolin JKS da majalissar gudanarwar kasar Sin, sun fitar da ka’idojin zaburar da sauyi, zuwa ci gaba maras gurbata muhalli a dukkanin fannonin raya tattalin arziki, da bunkasa zamantakewar al’umma.
Bisa tanadin ka’idojin da aka fitar a baya bayan nan, manyan burikan kasar su ne ya zuwa shekarar 2030, Sin za ta cimma manyan nasarori a fannin sauya akala zuwa ci gaba maras gurbata muhalli, a dukkanin fannonin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma, kana ya zuwa shekarar 2035, kasar za ta cimma nasarar gina tsarin raya tattalin arziki maras gurbata muhalli, bisa fitar da karancin iskar carbon, tare da cimma nasarar gina kasar Sin mai kayatarwa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)