A yau Talata ne ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wani kundi mai kunshe da matsayin kasar dangane da kudurin MDD mai lamba 2758. Kundin ya bayyana cewa, a ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 1971, da babban rinjaye taron MDD na 26 ya zartar da kuduri mai lamba 2758, wanda a cikinsa aka fayyace mayar da dukkanin hakkoki ga janhuriyar jama’ar kasar Sin, da amincewa da wakilan janhuriyar jama’ar kasar Sin a matsayin wakilan kasar Sin kadai a hukumomin MDD.
Wannan kundi ya kuma fayyace komai dalla-dalla, tare da warware batun wakilcin Sin, ciki har da batun yankin Taiwan, a dandalin MDD a mahanga ta siyasa, da shari’a, da matakan aiwatarwa. Kuma tabbas halasci, da inganci, da ikon mulkin kai na Sin ba zai taba sauyawa ba. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp