A yau Litinin ne gwamnatin kasar Sin ta fitar da kundin koli na farko a shekarar nan ta 2023, mai kunshe da manufofin raya karkara, kundin ya kunshi ayyuka 9, wadanda za su ingiza bunkasa karkara a wannan shekara ta bana.
Kundin ya kunshi matakan daidaita sarrafawa, da samar da hatsi da muhimman albarkatun gona, da karfafa gina muhimman ababen more rayuwa masu nasaba da ayyukan noma, da karfafa tallafin kimiyyar noma, da fasahohi da kayayyakin aiki, da kara fadada nasarorin da aka cimma a fannin yaki da fatara, da yayata manufar ci gaba mai inganci a fannin masana’antun karkara, da zurfafa dabarun da za su baiwa manoma karin kudaden shiga ta yadda za su samu wadata.
Kaza lika, matakan za su ingiza samar da yanayi mai inganci a fannin gudanar da kasuwanci, da kafuwar kauyuka masu kayatarwa, da bunkasa tsarin gudanar da jagoranci karkashin shugabancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da karfafa manufofi da tsare-tsaren inganta kirkire- kirkire.
Cikin kundin bayanin na farko da gwamnatin kasar Sin take fitarwa a ko wace shekara, ana fayyace manufofin dake kan gaba. Kuma ayyukan raya noma da karkara, na kan gaba a ajandar kasar Sin cikin shekaru 20 a jere, tun daga shekarar 2004. (Saminu Alhassan)