A yau Litinin, gwamnatin kasar Sin ta fitar da wani daftari da ya bayyana matakan zamanantar da sana’ar hada-hadar kayayyaki nan da shekaru biyar masu zuwa.
A cewar daftarin, kasar tana so ta samar da tsarin hada-hadar kayayyaki na zamani wanda zai kunshi ayyuka da kayayyaki masu inganci irin wanda zai zama na zamani, mai gamsarwa kuma mara gurbata muhalli nan da shekarar 2029.
Domin zamanantar da bangaren sana’ar, za a yi kokarin ingantawa da sabunta sassan da suka shafi wuraren ajiya, shagunan sayayya, manyan kantuna da kananan kasuwanni na unguwa, kamar yadda daftarin wanda aka fitar na hadin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati bakwai, ciki har da maaikatar cinikayya ya bayyana. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)