Hukumar kula da nukiliya ta kasar Sin ta bayyana cewa, kasar Sin ta kaddamar da wani bangare mai muhimmanci na aikin samar da makamashin nukiliya mafi girma a duniya, wanda ake kira “rana da ba na hakika ba” ko na wucin gadi mafi girma a duniya.
A cewar hukumar dake tsara wannan aiki, cibiyar nazarin kimiyar Physics ta SouthWestern Institute karkashin hukumar nukiliya ta kasar, an kammala samar da managartan matakai bangon farantan tattara zafi na farko dake daidaida zafin da ake bukata ko ITER a takaice, inda karfinsa ya zarce girman bukatun da aka kera, saboda haka ya dace da samar da galibin abubuwan da ake bukata. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)