Kasar Sin ta fitar da shirin kyautata muhalli domin inganta kiwon lafiyar al’umma na shekaru biyar, wanda zai gudana tsakanin shekarar nan ta 2025 zuwa 2030.
Hukumar kandagarki da shawo kan cututtuka ta kasar ko NADPC, da hadin gwiwar wasu sassa masu ruwa da tsaki ne suka fitar da shirin, wanda karkashinsa aka tanadi wasu muhimman matakai 16, na cimma nasarar samar da muhalli mai korayen tsirrai, da tsaro da ingancin yanayin rayuwar jama’a.
Kazalika, matakan sun kunshi karfafa gwiwar jama’a da su rungumi cin abinci mai gina jiki, da yawaita motsa jiki, da tsarin ware nau’o’in bola, da fadada yawan wurare masu tsirrai da na yin tattaki. Har ila yau, shirin ya kunshi inganta dinke manufofin da sauran sassa masu nasaba, da karfafa sanya ido, da tantance yanayin hadurra, da na gaggauta gabatar da gargadin aukuwar bala’u masu shafar lafiyar jama’a.
An tsara cewa ya zuwa shekarar 2030, shirin zai haifar da muhimman sakamako biyu, wato kyautata samar da ruwan sha mai inganci, da kara wayar da kan jama’a game da muhalli da kiwon lafiya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp