A Talatar nan ne ofishin yada bayanai na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani game da batutuwan da suka shafi sinadarin Fentanyl. Takardar mai taken “Shawo kan sinadarai masu alaka da sinadarin Fentanyl-Gudummawar kasar Sin.” Ta yi fashin baki game da yadda a ‘yan shekarun baya bayan nan, kasar Sin ke ta kara dora muhimmanci kan matakan shawo kan bazuwar sinadarai dangin Fentanyl, kana take ta karfafa hadin gwiwa da sauran sassan kasa da kasa, wajen dakile bazuwar miyagun kwayoyi, da zurfafa hadin kai da sauran kasashe masu ruwa da tsaki, ciki har da Amurka, wajen shawo kan bazuwar sinadarai dangin Fentanyl, da sinadaran da ake samar da shi daga gare su, inda kuma aka cimma manyan nasarori kan hakan.
Har ila yau, takardar bayanin ta yi nuni ga yadda Sin ke yayata manufar taimakawa juna tsakanin kasashe daban daban, tare da nuna adawa da zargin juna, da kaucewa daukar alhaki. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp