Kwanan baya, kwamitin kula da aikin lantarki na duniya (IEC) ya gabatar da ka’idar sarrafa mutum-mutumin inji mai kula da tsoffi. Ka’idar da kasar Sin ta ba da jagorancin tsarawa, ta tabbatar da yadda za a tsara da sarrafa mutum-mutumin injuna masu kula da tsoffi bisa halayen da tsoffi suke ciki, ta kuma tabbatar da yadda za a gudanar da bincike kan mutum-mutumin inji, yayin ba da izini gare su. Lamarin da ya ba da tabbaci ga bunkasuwar aikin sarrafa mutum-mutumin injuna masu kula da tsoffi yadda ya kamata.
Bayanin ya nuna cewa, an tsara ka’idar bisa bukatun tsoffi a fannonin samun kulawa cikin harkokin yau da kullum, da kiwon lafiya da dai sauransu. Haka kuma, ana fatan tsara mutum-mutumin inji bisa mabambanta bukatu, ban da ingancinsu, da tsimin makamashi, ana kuma fatan za su iya sa ido kan lafiyar jiki, da gudanar da harkokin gaggawa yadda ya kamata, tare da tuntubar iyalan tsoffi da masu ba da jinya cikin lokaci da dai sauransu. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp