Jiya Litinin, kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya sanar da cewa, a bana, kasar Sin za ta gaggauta aikin gyara da kyautata ababen aikin gona a muhimman yankunan shuka kayan lambu cikin manyan rumfuna.
A matsayin muhimmin matakin kara bukatun al’umma da karfafa bunkasar tattalin arziki, majalisar gudanarwar kasar Sin ta fara aikin kyautata na’urorin aiki da kuma maye gurbin tsoffin kayayyaki da sabbabi a bara. A bana kuma, an habaka wannan aiki zuwa harkar noma, inda za a mai da hankali wajen gyara da kyautata tsoffin manyan rumfuna masu aiki da hasken rana, da rumfuna na roba, domin karfafa tsarin kiyaye tsaro, da kara yin amfani da gonaki.
Haka kuma, bisa wannan shiri, za a kyautata da kuma samar da na’urorin zamani, kamar na’urar daidaita yanayi cikin rumfa, da na’urar samar da ruwa da taki mai sarrafa kanta da dai sauransu, ta yadda za a kara yin amfani da manyan injunan aikin gona masu sarrafa kansu, yayin da tabbatar da dauwamammen ci gaban aikin gona. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp