Maaikatar kula da harkokin ruwa ta kasar Sin ta bukaci a ci gaba da daukar nauyin yaki da balaun ambaliya da fari a zahirance, da inganta kwarewar tsara manufofi da ba da umurni ga ayyukan yaki da balaun, da kuma kyautata tsarin aikin yaki da su.
Maaikatar ta bayyana haka ne cikin wasu shawarwarin da ta fitar a kwanan nan, dangane da gaggauta gina tsarin gudanar da ayyukan yaki da balaun ambaliyar ruwa da fari.
Shawarwarin sun kuma bayyana cewa, ya kamata a ci gaba da horas da kwararru, da kara amfani da fasahohin zamani, don bada kyawawan nasihohi ga masu yanke shawara a wannan fanni. Kaza lika, ya dace a fidda sakon gargadi yadda ya kamata, da gaggauta aiwatar da matakai a zahirance, da tabbatar da bada umurni da aiwatar da shi ba tare da cikas ba. (Murtala Zhang)