Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya jadadda cewa, Taiwan wani bangare ne na kasar Sin tun a zamanin da, ba wai kasa ba.
Wang Wenbin ya bayyana haka ne yau Litinin yayin taron manema labarai na kullum, inda yake tsokaci game da yadda wasu Amurkawa ke ci gaba da yin furucin da ya sabawa kudurin MDD mai lamba 2758, yana mai cewa, wannan matsala ce da tuni kasashen duniya suka warware ta.
- Wang Yi: A Tsaya Kan Manufar Kasancewar Kasar Sin Daya Tak Don Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yankin Mashigin Teku Na Taiwan
- Yadda Nake Iya Aika Sako Ta Hanyar Rubuta Labari Yana Saka Ni Nishadi – Mardiyya
Game da sanya manufar kasar Sin daya tak da kasashen Larabawa suka yi cikin kudurin babban taron kungiyar kasashen, Wang Wenbin ya ce kasashen na Larabawa sun nuna cikakken goyon baya ga dokokin MDD da ma na huldar kasa da kasa.
Ya kara da cewa, ko a baya bayan nan, wata jami’ar majalisar kare hakkin bil adama ta MDD ta ziyarci kasar Sin, inda ta bayyana cewa, takunkuman da wasu kasashe suka yi gaban kansu wajen kakabawa kasar Sin sun keta dokokin kasa da kasa, kana za su yi mummunan tasiri kan hakkokin bil adama. Tana mai cewa, ya kamata wadancan kasashe su cire takunkuman da suka kakabawa kasar Sin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)