A yau Alhamis ne aka kaddamar da taron kasa da kasa, na karawa juna sani karo na 3, game da bunkasa cin gajiya daga tsarin hidimar ba da jagorancin taswira, daga tauraron dan adam na BeiDou na kasar Sin, ko BDS a takaice.
An bude taron na yini biyu ne a birnin Zhuzhou, na lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin, da nufin bunkasa masana’antar wannan fasaha, ta hanyar fadada sassan cin gajiya, da karfafa hadin gwiwar kasa da kasa a fannin.
Taron ya hallara sama da mahalarta 1,800, da suka hada da Sinawa da baki ‘yan kasashen waje masu bincike, da masu sana’o’i da jami’ai. Kaza lika, masu baje hajoji sun kafa runfuna don bayyanawa mahalarta taron sassan cin gajiyar tsarin na BDS, a fannonin rayuwa daban daban, ciki har da amfani da shi a hidimomin jigilar kayayyaki, ta amfani da na’urori masu kwakwalwa, da ababen hawa masu amfani da yanar gizo.
An kirkiri tsarin hidimar ba da jagorancin taswira daga tauraron dan adam na BeiDou, ko BDS ne a shekarar 1994. An kuma kammala gina tsarin BDS-1 a shekara ta 2000, da BDS-2 a shekarar 2012. Kaza lika, bayan kammala gina tsarin BDS-3, aka kuma fara aiki da shi a ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2020, Sin ta zama kasa ta 3 a duniya, da ta mallaki tsarin hidimar ba da jagorancin taswira daga tauraron dan adam na kashin kan ta tsakanin kasashen duniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp