Daga jiya Litinin zuwa yau Talata ne, kasar Sin ta gudanar da babban taron koli na raya tattalin arziki na shekara-shekara a birnin Beijing, fadar mulkin kasar, yayin da shugabannin kasar suka yanke shawara kan fannonin da za a ba da fifiko a kai a shekarar 2024.
Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin JKS, shugaban kasar Sin, kuma shugaban kwamitin koli na sojan kasar, ya gabatar da muhimmin jawabi a gun taron.
- Xi Jinping Ya Isa Hanoi A Ziyarar Aiki Da Ya Fara A Kasar Vietnam
- ECOWAS Ta Shimfida Sabbin Ka’idoji Domin Janye Wa Nijar Takunkumi
A yayin taron, an bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya samu farfadowa, inda aka samu ci gaba mai inganci a shekarar 2023.
Taron ya bayyana cewa, kasar Sin na bukatar shawo kan wasu matsaloli da kalubale, don kara farfado da tattalin arzikin kasar.
A cewar taron, baki daya, yanayi mai kyau ya zarce abubuwan da ka iya kawo cikas ga ci gaban kasar Sin, kuma tushen tsarin farfadowar tattalin arziki da kyakkyawan hangen nesa na dogon lokaci bai canza ba, yana mai kira da a kara nuna tabbaci.(Ibrahim)