Hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da ’yan sama jannati ta kasar Sin ko CMSA a takaice, ta ce an yi nasarar harba kumbon dakon kayayyaki na Tianzhou-8, kuma tuni kumbon ya hade da tashar binciken samaniya ta Sin wato Tiangong.
CMSA ta ce an harba kumbon ne da karfe 2:32 na daren Jumma’a bisa agogon birnin Beijing, kuma an turke kumbon a karshen sashen Tianhe, wato babban bangaren tashar binciken samaniya ta Sin wato Tiangong, wanda hakan ya kawo karshen aikin da aka tsara a wannan fanni.
- Yadda Gwamna Nasir Idris Ya Daura Damarar Bunkasa Ilimi A Jihar Kebbi
- Katsewar Lantarki: Masu Masana’antu Sun Kashe Naira Biliyan 238.3 Wajen Samun Wuta
An tsara cewa, ’yan sama jannatin kasar Sin na kumbon Shenzhou-19 da tuni ke cikin tashar samaniyar za su shiga kumbon Tianzhou-8, domin kwashe kayayyakin da kumbon ya isa da su tashar kamar yadda aka tsara.
Harba kumbon Tianzhou-8 a ranar Jumma’a shi ne karo na 3 da aka yi aikin jigilar kayayyaki zuwa tashar Tiangong, tun bayan fara aiwatar da matakan gudanar da ayyuka, da bunkasa tashar samaniya ta Sin. Kazalika shi ne aikin harba kumbuna karo na 546, da aka yi amfani da rokar Long March wajen aiwatarwa. (Saminu Alhassan)