Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adam da ake iya sabunta amfani da shi, ta amfani da rokar Long March-2F, daga cibiyar harba kumbuna ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar.
An harba tauraron dan Adam din ne a jiya Alhamis, ya kuma shiga falakinsa kamar yadda aka tsara, kuma za a yi amfani da shi wajen gudanar da gwaje-gwaje na tsawon lokaci a samaniya, kafin daga bisani ya dawo wani wuri na musamman a kasar Sin da aka tsara saukar sa.
Yayin da yake sararin samaniya, ana sa ran tauraron zai tantance wasu gwaje gwaje, game da fasahohi da kimiyyar samaniya da ake iya sabuntawa, ta yadda hakan zai samar da zarafin cin gajiya daga ayyukan sama jannati na zaman lafiya. (Saminu Alhassan)