A yau Alhamis ne kasar Sin ta harba tauraron dan adam zuwa sararin samaniya daga cibiyar harba tauraron dan adam ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin.
An harba tauraron dan adam na Fengyun-3 06 da karfe 11:47 na safe, agogon Beijing, da wata roka ta Long March-4C, ya kuma shiga cikin falaki kamar yadda aka tsara.
Wannan ne karo na 481 na ayyukan harba tauraron dan adam da nau’in rokar Sin mafi girma wato Long March. (Mai Fassara: Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp