Da karfe 4 na asubahin yau Talata bisa agogon Beijing, kasar Sin ta yi nasarar harba wani tauraron dan adam mai suna Shijian-25, ta amfani da rokar Long March-3B.
An harba tauraron ne daga cibiyar harba kumbuna ta Xichang dake lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar Sin, ya kuma shiga falakinsa kamar yadda aka tsara.
- Cece-kuce Kan Badaƙalar Kuɗaɗe A NNPCL: SERAP Ta Bukaci Mele Kyari Ya Yi Bayani
- Gwamnan Kano Ya Nemi A Rage Kuɗin Hajjin 2025
A cewar cibiyar nazarin zirga-zirgar kumbuna ta Shanghai, wadda ita ce ta kera tauraron na Shijian-25, za a yi amfani da shi a aikin tantance tsarin sake zuba makamashi, da fasahohin tsawaita wa’adin aiki masu nasaba.
Wannan ne karon farko da kasar Sin ta harba tauraron dan adam a shekarar nan ta 2025, kana karo na 555 da kasar ke amfani da rokar Long March wajen harba taurarin dan adam. (Saminu Alhassan)