Kasar Sin na kara aiwatar da matakan inganta hidimomin kiwon lafiya a kananan asibitocin al’umma, da yankunan karkara, yayin da bikin bazara na al’ummar kasar ke kara karatowa, domin tabbatar da nasarar kandagarki da shawo kan cutar COVID-19, wadda aka iya fuskantar bazuwar ta sakamakon bikin na gargajiyar Sinawa.
Da take karin haske game da hakan, jami’ar hukumar kiwon lafiyar kasar Jiao Yahui, ta ce wadannan cibiyoyin kiwon lafiya na daukar matakai daban daban, na karfafa hidimar ma’aikata, tare da tanadar isassun magunguna da za a iya bukata.
Jiao ta ce an umarci asibitoci dake matsayi na 3 a biranen kasar, da su kafa tsarin sadarwar kai tsaye, na tsawon yini da kwana tsakanin su da kananan asibitoci dake yankunan karkara domin tallafawa ayyukan su.
Asibitoci masu matsayi na 3, su ne asibitocin kwararru na kasar Sin masu adadin gadajen kwantar da marasa lafiya mafiya yawa, da kuma kayan aiki isassu kuma na zamani.
A bana bikin bazara na gargajiyar kasar Sin, ko bikin sabuwar shekarar Sinawa, ya fado a ranar Lahadi 22 ga watan Janairun nan. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa)