Hukumomin kasar Sin sun fitar da wata takarda, da nufin ci gaba da inganta manufofin inshorar likitanci, domin saukaka kudaden da masu fama da cutar COVID-19 ke kashewa.
Takardar wacce hukumar kiwon lafiyar kasar da wasu sassa uku suka fitar cikin hadin gwiwa, ta nuna cewa, duk masu fama da cutar COVID-19, za su samu tallafi daga gwamnati, don biyan kudaden jinyar asibiti da ba ya cikin tsarin inshorar lafiya,da inshorar cututtuka masu tsanani, ko asusun taimakon lafiya, idan har sun kwanta a asibiti kafin ranar 1 ga watan Afrilun,shekarar 2023.
Marasa lafiya da ke da inshorar lafiya, za su samu abin da bai gaza kasa da kashi 70 na kudaden da ake kebewa majinyata da kuma maganin kamuwa da cutar COVID-19 na gaggawa a cibiyoyin kiwon lafiya da aka kebe da aka biya tun daga ranar 31 ga Maris .(Ibrahim)