A jiya Juma’a 2 ga watan Yunin nan ne kwamitin tsaron MDD, ya amince da kudurin tsawaita wa’adin aikin tawagar tallafin jin kai dake aiki a kasar Sudan, zuwa ranar 3 ga wayan Disambar karshen shekarar nan.
Da yake tsokaci game da hakan, mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya ce manyan burikan sassan kasa da kasa su ne wanzar da zaman lafiya da daidaito a kasar Sudan. Kuma Sin na jaddada kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a rikicin kasar, da su gaggauta dakatar da bude wuta, tare da kawo karshen yakin da suke gwabzawa.
Geng Shuang, ya kara da cewa, ya kamata sassan da batun ya shafa su warware dukkanin sabani, da bambance-bambancen dake tsakanin su ta hanyar siyasa, su kuma samar da yanayi na cimma burin dakatar da bude wuta mai dorewa, da kuma tsare-tsaren siyasa. (Saminu Alhassan)