Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang yi ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo a babban taron kwamitin kare hakkin dan Adam na majalisar dinkin duniya karo na 58 da ya gudana a ranar Litinin, inda ya jaddada aniyar kasar Sin na yin aiki tare da dukkan kasashen duniya wajen tabbatar da sahihin ra’ayi game da kare hakkin dan Adam, da kira ga yin gyare-gyare da kyautata tsarin gudanar da harkokin da suka shafi kare hakkin dan Adam a duniya.
Wang ya ce yana da matukar muhimmanci a tuna da ainihin manufar gudanar da ayyukan kare hakkin dan Adama, wadanda suke maida hankali kan bukatu da kyautata zaman rayuwar jama’a.
- LEADERSHIP HAUSA Ta Bayyana Waɗanda Suka Yi Nasara A Gasar Gajerun Labaran Soyayya
- Ba Ni Da Sha’awar Takarar Shugaban Ƙasa A 2031 – Nuhu Ribadu
Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin na matukar kin amincewa da ayyukan da ke katsalandan a harkokin cikin gidan wasu kasashe ta hanyar fakewa da kare hakkin dan Adam, wadanda ke yin watsi da ‘yancin kasa, da tsaro da kuma kare rayukan jama’a.
Wang ya kara da cewa, “Dole ne a tabbatar da daidaici da adalci, sannan a ba da fifiko ga ‘yancin rayuwa da samun ci gaba a matsayin muhimman hakkokin bil Adam.” Kazalika, dole ne a yi watsi da ka’idojin da ke nuna bambanci da wariya a batutuwan da suka shafi kare hakkin dan Adam.
Daga karshe Wang ya ce, a shirye kasar Sin take ta yi aiki tare da sauran kasashen duniya, don tabbatar da duniya mai tafiya da zamani kuma mai ci gaba cikin lumana, da hadin gwiwar moriyar juna, da samun wadata tare. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp