Kasar Sin ta kaddamar da wani shiri na gwaji na samun basussukan kasashen waje da za a sarrafa su a sashen makamashi mai tsafta, a wani yunkuri na kara jawo jarin duniya ga fannin ayyukan samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba na kasar.
A yau Alhamis, hukumar kula da musayar kudaden waje ta kasar Sin (SAFE) ta bayyana cewa, an yi tsarin shirin na gwaji ne a yankuna da birane 16 da suka hada da Shanghai, da Beijing, da Hebei da kuma Qingdao, kuma ana karfafa gwiwar kamfanonin da ba na hada-hadar kudi ba, su yi amfani da kudaden na kasashen waje wajen gudanar da ayyukan da suka shafi amfani da makamashi mara gurbata muhalli. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp