Wani mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce kasar sa ta kadu, tare da Allah wadai da harin da aka kaiwa asibitin Ahli Arab dake Gaza, wanda ya haifar da asarar rayukan fararen hula masu tarin yawa.
Kakakin ya ce Sin na mika sakon ta’aziyyar rasuwar mamatan, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata. Kaza lika Sin na kira da a gaggauta dakatar da bude wuta, da kawo karshen yaki, kana a yi duk mai yiwuwa wajen kare rayukan fararen hula, domin kaucewa fadawa mummunan yanayi na jin kai. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp